Mr. Liu ya bayyana cewa, tawagar wakilan kasar Sin ta gano cewa, kararrakin da aka gabatar wa koton kula da harkokin teku ta duniya na ci gaba da karuwa, kuma fannonin da kararrakin suka shafa sun karu, yayin da tasirinsu suka habaka cikin kasa da kasa, lamarin ya nuna cewa, an riga an shiga wani sabon matsayi wajen daukar nauyin yarjejeniyoyin da abin ya shafa bisa dukkan fannoni. Tawagar kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan koton da ta ci gaba da aikinta na warware rikicin da suka shafi harkokin teku cikin lumana, kiyaye dokokin kula da harkokin teku na kasa da kasa da kuma inganta dokar kula da harkokin teku ta duniya da sauran fannoni, kuma Sin ta nuna yabo ga kotun bisa ga babban taimako da ta bayar ga kasashe masu tasowa.
Haka zalika, Mr. Liu ya kara da cewa, tawagar kasar Sin ta amince da shawarar aikin da kungiyar musamman mai kula da harkokin nazarin rayuwar halittun teku wadanda ba su karkashin mallakar ko wace kasa ba ta gabatar a babban taron MDD. Sin na ganin cewa, harkokin yankunan karkashin tekun da ba mallakar kowa ba da kuma tekun kasa da kasa na shafar moriyar gamayyar kasa da kasa, gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin nazarin rayuwar halittun teku yadda ya kamata na da muhimmiyar ma'ana ga aikin kiyaye dokokin tekun kasa da kasa bisa adalci da zaman lafiya. (Maryam)