A wajen sauraron shari'ar, Mohamed Morsi ya jaddada halaltaccen matsayinsa na shugaban da jama'ar kasar suka zaba. Daga baya, lauyoyin da ke kare shi sun bar wurin tare da barazanar yin murabus, don nuna rashin amincewa da yadda aka kulle Morsi da wasu sauran mutane cikin kananan dakunan gilashi na ihun ka banza yayin da ake sauraron shari'arsu. Wasu manyan kusoshin kungiyar 'Yan Uwan Musulmi sun yi ihun kalaman kin jinin sojojin kasar a wurin shari'a, tare da buga gilashin da aka yi amfani da shi don kebe Morsi, lamarin da ya haifar da rudani. A karshe dai babban alkali mai sauraron shari'ar ya sanar da dakatar da sauraron shari'ar zuwa mako mai zuwa. An ce idan aka tabbatar da cewa Morsi da mutanensa sun aikata laifin cin amanar kasa, za a iya kai ga yanke musu hukuncin kisa. (Bello Wang)