Wadannan kararraki guda biyu da aka daukaka sun danganci ka'idoji da tsarin da aka bi wajen zabar mambobin majalisar wakilan kasar ta Masar, watau kwamitin tsara kundin mulkin kasar na majalisar taron jama'ar kasa wanda aka jingine shi a shekarar da ta gabata.
A watan Yuni na shekarar 2012, babbar kotun Masar ta sanar ta rushe majalisar wakilan kasa da aka zaba tsakanin karshen shekarar 2011 da farkon shekarar 2012, sakamakon sabawa tsarin mulkin kasar da aka yi yayin da take gudanar da ayyukan ta.
Daga bisani kuma, an nuna shakku game da mambobi dari na kwamitin tsara kundin mulkin kasar, wadanda majalisar wakilai ta zaba, duk da haka, a karshen shekarar 2012, an cimma nasarar zartas da tsarin mulkin kasa da kwamitin ya samar, tare da samun kuri'un amincewa kimanin kashi 60 bisa dari.
An rawaito maganar wani masanin doka dake cewa, zartas da tsarin mulkin kasar bisa kuri'ar raba gardama ta dukkanin jama'ar kasar, na iya wanke kwamitin da ya tsara wannan kundi daga tuhumar ko wace irin kotu dake kasar ta Masar. (Maryam)