in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta dauki alhakin harin boma-boman da aka kai ma kasar Masar
2014-01-25 20:24:30 cri
Wata kungiyar mai tsattsauran ra'ayi mai taken 'Ansar Bait Magdis' ta sanar a shafin internet a ranar Asabar din nan, cewa ita ta kai harin boma-boman a birnin Alkahira da wasu yankunan dake kewayensa a ranakun Juma'a da Asabar din nan.

Kafin haka, kungiyar ta sanar a ranar Juma'a cewa, ita ce ta kai harin bom a babban ofishin hukumar tsaron birnin Alkahira a wannan rana, haka zalika ta yi kashedi ga jama'ar kasar da kada su halarci bikin taya murna da sojojin kasar suka gudanar a ranar Asabar.

A ranar Juma'a 24 ga wata, an kai harin bom har karo 4 ga ofisoshin hukumar tsaro dake Alkahira da Giza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, da raunatar wasu kusan dari daya. Daga bisani a safiyar ranar Asabar din nan, an samu tashin bom a wata makarantar horar da 'yan sanda dake gabashin birnin Alkahira, inda mutum daya ya ji rauni. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China