Kamfanin dillancin labarun kasar ta Masar MENA ya fidda wannan labari, yana mai cewa duka duka, mutane 545 ne aka gurfanar gaban kotun, kafin daga bisani a wanke 17 daga cikin su. Har wa yau cikin wadanda aka tuhuma, mutane 154 ne kadai suke hannu, yayin da sauran ba su kai ga shiga hannu ba tukuna.
Tun da fari an zargi wadannan mutane 545 ne da kai hari ga wani ofishin 'yan sanda, da sauran hukumomin dake lardin Minya a watan Augustan da ya gabata, inda suka kashe mataimakin shugaban ofishin 'yan sandan, da cinna wuta, tare da kwace makaman 'yan sanda, da kuma yin harbin kan mai uwa da wabi.
Kafin yanke hukuncin, sai da kotun ta saurari shaidun gani da ido, daga bisani yayin zamanta na biyu a ranar 24 ga wata, ta yanke hukuncin kisa ga mutane 528. Sai dai lauyoyin wadanda ake zargin sun bayyana matakin da kotun ta dauka da karya doka, bayan da a cewarsu ta yi watsi da shawarwarin da suka gabatar mata.
Bisa dokokin kasar Masar, za a jira amincewar babban mai shari'ar birnin Alkahira, kafin a tabbatar da hukuncin kisa. Don haka za a ci gaba da tsare wadannan mutane 528, yayin da su ma suke da damar daukaka kara.
Wani reshen kungiyar ta 'yan uwa musulmi dake Birtaniya ya yi fatali da wannan hukunci, tare da yin Allah wadai da shi, yana mai kira ga masu goyon bayan kungiyar da su gudanar da zanga-zanga a sassan kasar Masar daban daban. (Bello Wang)