in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa masu yawon bude ido a Masar
2014-02-17 15:27:02 cri
Kwamitin sulhun MDD ya ba da wata sanarwa a ranar Lahadi 16 ga wata, inda ya yi Allah wadai da harin bam din da aka kai wa motar bas dai da ke dauke da 'yan yawon shakatawa a zirin Sinai na kasar Masar ranar Lahadi, inda ya yi kira da a yi kokarin kama mutanen da suka kai harin don gurfanar da su a gaban kotu.

An kai harin ta'addanci ne a ranar Lahadi kan motar bas din da ke dauke da masu yawon bude ido a kudancin Sinai na kasar Masar, harin da ya haddasa mutuwar mutane 4, ciki har da direban motar da masu yawon shakatawa 'yan kasar Koriya ta Kudu guda uku yayin da wasu da dama suka jikkata.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China