in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana ta yaba da gudummawar da Sin ke bayarwa wajen yaki da cinikin hauren giwa
2014-02-27 14:18:06 cri

Shugaban kasar Botswana Ian Khama, ya jinjinawa babbar gudummawar da kasar Sin ke bayarwa, wajen yakin da ake yi da haramtaccen cinikin nan na hauren giwaye.

Shugaba Khama ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, cikin wani takaitaccen bayani da ya gabatar ga al'ummar kasarsa, don gane da sakamakon taron tattauna batun haramcin cinikayyar namun daji, wanda ya halarta a birnin Landan.

Khama ya ce, ko da a ranar 6 ga watan Janairun da ya gabata, sai da mahukuntan kasar ta Sin suka kwace, tare da lalata tan 6 na hauren giwaye, a matsayin wani mataki na dakile wannan haramtaccen ciniki.

Haka zalika, a shekarar da ta gabata, yayin da kasar ta Botswana ta kira taro na musamman dangane da rayuwar giwaye, kasar ta Sin ta alkawarta zage damtse, wajen yin aiki kafada da kafada, da sauran kasashen duniya wajen dakile cinikayyar hauren giwa.

Bugu da kari shugaba Khama ya ce, ko da a taron na birnin Landan, sai da Sin ta alkawarta ci gaba da yakin da, tare yin da cinikayyar hauren giwaye, da kuma farauta ba bisa ka'ida ba.

Kasar Botswana wadda ke da sama da giwaye 200,000, ta kasance mafi yawan giwaye a nahiyar Afirka. A kuma shekarun baya bayan nan ta dukufa kwarai, wajen daukar matakan hana farautar namun daji, ciki hadda dokar dakatar da lasisin farauta tun daga watan Janairun bana. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China