in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta amsa tambaya game da yaki da fasakwaurin hauren giwa
2014-02-14 16:19:13 cri

Yayin taron manema labaru da ya gudana a ranar 13 ga watan nan,  kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, tana fata masu ruwa da tsaki za su lura da kokarin da kasar Sin ta ke yi cikin adalci, a fagen yaki da fasa kwaurin hauren giwa ta barauniyar hanya, tare da nasarorin da aka samu.

Don gane da wasu rahotanni da manema labaru suka ruwaito, dake nuna yadda kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya ke cewa, ya dace kasar Sin ta ci gaba da kara kokarin yaki da fasa kwaurin hauren giwa ta barauniyar hanya, Hua Chunying ta ce, a ko da yaushe kasar Sin na tsaiwa tsayin daka, wajen daukar matakan kiyaye rayukan dabbobin daji, ciki hadda giwaye.

A farkon wannan shekara ma, kasar Sin ta lalata hauren giwa da yawansu ya kai Ton 6.1, da ta kwace daga hannun masu fasa kaurin sa ta barauniyar hanya, matakin da ya nuna cewa, gwamnatin Sin tana adawa da yin cinikin sassan dabbobin daji ba bisa ka'ida ba. Har ila yau hakan ya jaddada matsayin ta na hana ko wace kungiya, ko wani mutum ya ci moriyar cinikin dabbobi, ko sassan jikinsu ba bisa ka'ida ba.

Madam Hua ta ce, kasar Sin ta fitar da wasu dokoki, da tsarin bincike domin tabbatar da nasarar burin da aka sa gaba, baya ga hukumar da ke kula da tsaron jama'a, da hukumar kwastam, da hukuma mai lura da masana'antu da kasuwanci, wadanda suka ta tashi tsaye, wajen shiga hadin gwiwar kasa da kasa a aikin bincike. Wadannan matakai dai suna taimakawa wajen hana fasa kaurin hauren giwa.

Bugu da kari kasar Sin na kara himma wajen yaki da fasa kaurin hauren giwa, karkashin matakan da ke sahun gaba a dukkanin fadin duniya, kuma a nan gaba, Sin za ta ci gaba da bincike, da nufin shiga hadakar kasa da kasa domin cimma burin da aka sanya gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China