Tsakanin giwaye dubu 30 zuwa dubu 50 aka kashe a nahiyar Afrika a shekarar 2012, a cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba a Congo, ta hukumar Interpol da asusun kasa da kasa kan kare namun daji (IFAW) da suka kaddamar da aikin Wendi da ya shafi hukunta kungiyoyin da aikata manyan laifuffuka dake da hannun kan fataucin hauren giwa a Afrika.
A tsawon shekaru uku na baya bayan nan, an kashe giwaye da dama a Afrika. Akalla a shekarar 2012, giwaye dubu 30 zuwa dubu 50 aka kashe domin haurensu.
Haka kuma shekarar 2012 ta kasance mumunar shekara a fannin kama hauren giwa, tare da ton 34 na hauren giwa da aka kama ba bisa doka ba, wanda ya kasance adadi mafi girma da aka samu a cikin shekaru 24, tun lokacin da wadannan bayanai aka fara hakikance su. Adadin da ya wuce da kashi 35 cikin 100, bisa ga na shekarar 2011 dake ton 24,3, in ji hukumar Interpol da IFAW.
A cewar wadannan hukumomi, matsalar da giwaye ke fuskanta na kara tsananta a wannan lokaci fiye da shekarun da suka gabata, musammun ma tsakiyar Afrika da yammacin Afrika, a kasar Congo, Cote d'Ivoire, Liberiya da Guinee-Conakry. (Maman Ada)