in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin, Cameron da Merkel sun bayyana ra'ayi daya kan shawo kan tabarbarewar yanayi a Ukraine
2014-03-10 10:44:00 cri

Shugabannin kasashen Rasha, Birtaniya da Jamus sun nuna damuwarsu bai daya game da yadda za'a shawo kan tabarbarewar tashin hankalin da ke gudana a Ukraine, duk da kokarin da wassu yankuna ke yi na ballewa, in ji kamfanin dillancin labarai na fadar Kremlin a ranar Lahadin nan.

An ce, shugaban kasar Rashan Vladimir Putin, firaministan Birtaniya David Cameron, da kuma shugaba Angela Merkel ta Jamus suna cigaba da tattaunawa a kan yanayin da ke da rikirkitarwa matuka na siyasa da zamantakewar a kasar ta Ukraine, da kuma kuri'ar raba gardama da Crimea ke son kadawa a ranar 16 ga wata.

Wannan mataki da halatacciyar hukumar Crimea ta dauka yana kan dokar kasa da kasa, wadda kuma ta dauke shi ne domin kare martabar al'ummar ta, hukuma mai cin gashin kanta ta Ukraine da yanzu haka ta zama cibiyar takaddama a kasar kamar yadda shugaba Putin ya bayyana.

Putin ya ce, mahukuntan kasar ta Ukraine a yanzu haka ba wani abu da suke yin a shawo kan matsalar masu ikirarin 'yan kasa da kuma 'yan aware da ke faruwa a Kiev, da ma sauran sassa daban daban na kasar.

A wani labarin kuma Rasha ta amince da cewa, akwai banbancin ra'ayi wajen shugabannin game da duba yanayin da ake ciki a kasar da ke gabashin Turai. Don haka sun amince su cigaba da aiki tukuru na tuntubar juna, da ma tuntubar shugabannin huldar harkokin wajen kasashen nasu duka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China