Kasar Sin ta yi kira ga sassa daban daban na kasar Sham da su dakatar da yin musayar wuta a tsakaninsu cikin sauri, tare da ci gaba da shawarwari a tsakaninsu a birnin Geneva, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang yau ranar Talata 22 ga wata.
Ranar 21 ga wata, Mohamed Jihad Al Lahham, shugaban majalisar dokokin kasar Sham ya sanar da cewa, za a gudanar da babban zaben shugaban kasar a ranar 3 ga wata Yuni.
Dangane da hakan, Qin Gang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, ya kamata sassa daban daban na Sham su yi kokari tare wajen kaddamar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi wanda zai sulhunta a tsakanin sassa daban daban.(Tasallah)