Wani babban jami'in ma'aikatar tsaron kasar Amurka ya tabbatar da cewa, sojan Amurka sun fara duba yankin da za su kafa na'urorin kakkabo makamai masu linzami nan da dan lokaci a kasar Koriya ta Kudu.
An bayyana kafa tsarin kakkabo makamai masu linzami da Amurka ke burin yi a Koriya ta Kudu, a matsayin abin da ka iya haifar da babbar illa ga yanayin zaman lafiya a yankin Koriya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne, ya bayyana hakan jiya Laraba a nan birnin Beijing, yayin wani taron manema labaru.
Mr. Qin ya kara da cewa yanzu haka ana ci gaba da fuskantar matsaloli, a fannoni daban daban a zirin Koriya, kuma kasar Sin tana goyon bayan daukar matakan wanzar da zaman lafiya a wannan yanki, tare da burin hana yin amfani da makaman nukiliya a zirin, da kuma warware matsalolin zirin ta hanyar yin shawarwari. (Zainab)