in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu sakwanni daga jirgin ruwan da ya nutse ba, in ji 'yan sandan ruwa na Koriya ta Kudu
2014-04-19 16:54:49 cri
Yau Asabar 19 ga wata, hukumar 'yan sandan teku ta Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin aikin ceto kan jirgin ruwan fasinja Sewol da ya nutse amma kuma har zuwa yanzu ba a samu sakwanni daga wannan jirgin ruwan ba. Ya zuwa safiyar yau da misalin karfe 10, an tabbatar da mutuwar mutane 29, yayin da sama da mutane 270 suka bace, a ciki har da Sinawa 4.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana kuma, hukumar 'yan sandan teku na Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, ana cigaba da aiki karkashin ruwa bi da bi ba tare da kasala ba, domin lalube mutanen da suka lake cikin wannan jirgin ruwa. A safiyar yau, an samu ganin gawawwaki uku masu sanye da rigar ceto cikin jirgin, saidai kuma mawuyacin yanayi na kawo cikas wajen ci gaba da aikin ceto da na debo gawawwaki. Tun rana ta farko, masu aikin ceto suke kokarin aika sakwanni zuwa cikin jirgin ruwan, amma har zuwa yanzu, ba a samu martani ko kadan ba.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China