in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a hadarin jirgin ruwan koriya ta kudu ya karu zuwa 213
2014-05-01 16:08:56 cri
Bayanai daga koriya ta kudu na cewa, yawan mutane da suka mutu sanadiyar hadarin jirgin ruwan kasar da ya nutse ya karu zuwa 213.

Alkaluma na cewa, ya zuwa ranar Alhamis da rana,an tabbatar da mutuwar mutane 213,yayin da wasu 89 suka bace. Kuma har yanzu babu karin ko wani mutum da aka samu damar ceton shi tun lokacin da aka ceto mutane 174 daga teku bayan da jirgin ya kife a ranar 16 ga watan Afrilu.

Yayin da aka shiga kwanaki na 16 na aikin ceton mutane daga jirgin ruwan,gawar mutum guda kawai aka kara gano wa a rana guda daga jirgin da ya tsine bayan da igiyar ruwa da torokon ruwa suka haifar da tsaiko a aikin neman mutanen da ake yi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China