in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a hadarin jirgin ruwa Koriya ta Kudu ya kai 108
2014-04-25 20:47:38 cri
An ba da kiyasin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar nutsewar jirgin ruwan kasar Koriya ta Kudu, inda ya zuwa karfe ukun rana na Talatan nan 22 ga wata, suka kai 108 bayan kokarin aikin ceto da kwararrun nunkaya suke aiwatarwa domin neman mutanen da har yanzu ake sa ran sun makale a cikin jirgin.

An tabbatar da mutuwar mutanen 108 an kuma ceto wadansu 194 sannan sauran kuma sun bace ana kan nemansu, in ji Koh Myun-seok, babban darektan na'urori da fasaha a kan tsaron bakin tekun jiragen ruwan kasar.

Su dai wadanda aka ceto har yanzu ba a samu kari a adadinsu ba na 174. jirgin mai nauyin tan 6,825 ya kife ne tare da nutsewa a tsibirin Jindo dake kudu maso yammacin gabar kasar ta Koriya ta kudu a ranar Laraban da ta gabata yana dauke da mutane 476 da suka hada da daliban makarantar gaba da firamare na Danwon su 325 da kuma malamansu 14. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China