in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasu sanadiyyar nutsewar jirgin ruwan fasinja na Koriya ta Kudu ya karu zuwa 25
2014-04-18 10:28:12 cri
Bisa labarin da aka samu daga hedkwatar ba da shawarar tinkarar bala'i da hadari ta kasar Koriya ta Kudu, an ce, ya zuwa safiyar ranar 18 ga wata, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar nutsewar jirgin ruwan fasinjan na kasar ya karu zuwa 25, a yayin da wasu mutane 271 suka bace, yayin da aka ceto mutane 179.

Duk da cewa tun ranar 17 ga wata, kasar Koriya ta Kudu ta riga ta tura masu aikin ceto 500, ciki har da sojojin ruwa 229, amma matsalar tabarbarewar yanayi ya kawo tsekon gudanar da binkice a cikin wannan jirgi dake karkashin ruwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China