Ya kuma kara da cewa, 'yan ta'adda na son cimma mugun burinsu na siyasa ta hanyar kai hari a birnin Urumqi, amma dukkanin jama'ar kasar Sin ba za su yarda da burinsu da kuma matakan da suka dauka ba ko kadan. Dangane da haka, 'yan sandan kasar Sin na dukufa wajen gane harkokin wadanda suka kai wannan harin ta'addanci ya shafa, za su kuma bankado bayanan da abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)