A sa'i daya kuma, da babbar murya ne jami'ai da jama'ar wurin sun yi alla wadai da wannan harin ta'addanci mai tsanani, kana sun bayyana cewa, duk wani yunkurin lalata zaman karko a jihar Xinjiang zai bi ruwa.
Shugaban jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, Nur Bekri ya ba da jawabi ta kafar talabijin a wannan rana, inda ya yi suka sosai kan wannan danyen aiki da 'yan ta'adda suka aikata, kana ya nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon lamarin, ya kuma mika jajensa ga iyalansu, da kuma wadanda suka jikkata.
Mahmut Niyaz, wanda ke zaune a unguwar Tianshan ta birnin Urumqi ya ce, mun fusata tare da la'antar wannan mummunan aiki. Muna fatan gwamnatinmu za ta karfafa karfin yakar ayyukan ta'addanci, ta kama wadanda ke tsara ayyukan ta'addanci, da masu shiryawa, da kuma masu ba su taimako baki daya. (Bilkisu)