Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya buga wayar tarho ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, don nuna jajensa kan wannan harin ta'addanci, tare da bayyana cewa, da babbar murya ce kasar Rasha ke alla-wadai da wannan mummunan aikin. Putin yana mai cewa, ba shakka za a cafke masu tayar da kayar baya da masu hannu kan harin, domin hukunta su. Kaza lika shugaba Putin, ya bayyana burinsa na karfafa hadin kai tsakanin kasashen Rasha da Sin wajen murkushe ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.
A nasa bangaren, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa shi ma yayi kakkausar suka kan wannan harin ta'addanci a gaban manema labarai, tare da nuna ta'azziyar kasar Faransa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Ya bayyana cewa, kasar Farsansa tana daukar matsaya daya tare da gwamnatin Sin da jama'arta kan wannan masifar. (Bilkisu)