Za a shirya bikin nune-nunen ba da ilmi na kasar Afirka ta Kudu daga ranar 19 zuwa 21 ga wata. A ranar Lahadi 18 ga wata, wakilan jami'o'in kasar Sin sun shirya wani taro a birnin Johannesburg, don gabatar da nune-nunensu tare kuma da zantawa da manema labaru.
Bisa shirin da hukumar ba da tallafin karo ilimi ta ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta tsara, bikin nune-nunen zai samu halartar shugabanni da ma'aikatan jami'o'i 18 na kasar Sin, inda za su karbi dalibai daga kasar Afirka ta Kudu.
Wadannan jami'o'i suna fatan kafa hukumomin karbar dalibai a Afirka ta Kudu, inda za su iya kara karbar nagartattun dalilai daga kasar, a sa'i daga kuma za su iya samar da dama ga yaran Sinawa da ke zama a Afirka ta Kudu wajen dawowa kasar Sin don kara ilmi. (Danladi)