in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya taya murnar sabuwar shekara ga Sinawa
2014-01-30 10:14:34 cri

A gabannin sabuwar shekara ta kasar Sin, shugaban kasar Afirka ta Kudu Mista Jacob Zuma ya mika sakon taya murnar sabuwar shekara ta doki ta gargajiya ta Sin ga Sinawa da ke Afirka ta Kudu da kuma Sinawa a duniya baki daya, yana mai fatan Sinawa a ko ina zasu kasance cikin koshin lafiya.

Shugaba Zuma ya bayyana cewa, a halin yanzu dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta kara bunkasuwa, don haka wannan sabuwar shekara data kasance shekarar doki bisa kalandar gagajiya ta kasar Sin, yana fatan ganin alamar saurin tafiyar doki za ta sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Zuma wanda ya aika da sakon taya murna ga ofishin jakadancin Sin da ke Afirka ta Kudu da Sinawa da ke kasar baki daya ya ce, a kasar Sin doki ya kasance wata alama ce mai kyau,don haka yana fatan alamar zai kawo alheri ga ayyukan da za a gudanar a shekarar.

Mr Zuma har ila yau yayi nuni da cewa, Sin da Afirka ta Kudu sun inganta dangantakarsu, wadda take bunkasuwa cikin sauri. Sa'an nan wannan lokacin da ake taya juna murnar sabuwar shekara ta doki, shi ma lokaci ne da ake kokarin tsara shirye-shiryen kasashen biyu na sabuwar shekara. Yana fatan za'a dauki matakai masu karfi domin tsara wani babban shiri na kara raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China