A ran Alhamis 27 ga wata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya kimanta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, inda ya ce, dalilin da ya sa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu ya kara danko shi ne, domin an kafa shi ne bisa daidaici.
A lokacin da yake zantawa da wakilin tashar Afirka ta gidan talibijin din CNBC na Amurka, Mista Zuma ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana mayar da Afirka ta Kudu da sauran kasashen Afirka a matsayin abokai da ke nuna daidaici ga juna, amma kasashen yamma su kan mayar da Afrika a matsayin mallakar su.
Zuma ya kara da cewa, wani dalilin da ya sa ba a samu ci gaba daga dangantakar da ke tsakanin kasashen yamma da kasashen Afirka da aka yi ma mulkin mallaka ba shi ne, dangantakar su ba ta kafu bisa tushen daidaici ba, don haka ya yi suka ga kasashen yamma da ke nuna adawa da zuba jari a Afirka da Sin take yi.
A ganin Mr Zuma, ya kamata kasashen Afirka su kara samun 'yanci wajen raya dangantakarsu da sauran kasashen da ba na yammacin duniya ba, musamman dangantakar da ke tsakaninsu da kasashe da tattalin arzikinsu ke bunkasa,wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu BRICS.(Danladi)