Akwai dai alamu dake nuna cewa, kyakkyawan yanayin da ake ciki yanzu haka a kasar, zai dore har ya zuwa lokacin gudanar zabukan kasar na ranar 7 ga watan Mayu mai zuwa.
Ministan harkokin wajen kasar Lesotho, kuma jagoran tawagar kungiyar ta SADC Mohlabi Tsekoa ne ya bayyana hakan a birnin Pretoria, ya na mai cewa tawagar za ta sa ido ne ga yadda zaben zai wakana, ba tare da tsoka hannu cikin gudanar sa ba.
Tuni dai tawagar wadda ta isa birnin na Pretoria a ranar Alhamis, ta gana da daukacin sassan masu ruwa da tsaki game da wannan zabe. Ta kuma nuna gamsuwa da kokarin su game da burin cimma nasarar zaben dake tafe.
Daga nan sai ya nanata muhimmancin dake akwai, ga daukacin masu ruwa da tsaki su mai da hankali ga kalubalen dake fuskantar ci gaban kasar sama da kowace irin bukata. (Saminu Alhassan)