in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 36 sun mutu sakamakon rikici a tsakanin dakarun kabilar Tuareg da sojojin kasar Mali
2014-05-19 10:11:15 cri

Ministan tsaron kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya sanar a ranar Lahadi 18 ga wata cewa, a ranar Asabar dakarun kungiyar "National Movement for the Liberation of Azawad" wato MNLA da ta fi girma na kabilar Tuareg da ke arewacin kasar Mali sun kai farmaki ga sojojin kasar a birnin Kidal da ke arewacin kasar, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 36 tare da jikata wasu 87.

Ministan ya ce, yayin da sojojin kasar Mali suke gudanar da aikin tsaro dangane da ziyarar firaministan kasar Moussa Mara a Kidal, sun gamu da farmaki daga kungiyar MNLA da wasu 'yan ta'adda. A lokacin wannan gumurzu sojoji 8 sun mutu tare da jikata wasu 25. Sai dai a halin yanzu, ban da babban ginin babban yankin Kidal da ya rage, sojoji sun riga sun samu ikon sauran hukumomin gwamnati na Kidal.

Firaminista Mara ya isa Kidal don ziyara aiki a yammacin wannan ranar ta Asabar 17 ga wata, abin da ya zama karo na farko da ya ziyarci arewacin kasar tun darewarsa mukamin a watan Afrilu. Bayan da aka sanar da niyyar ziyarar Mara a Kidal, nan take kungiyar MNLA ta nuna adawarta. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China