Sanarwar ta ce, bayan rikicin, ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na M.D.D. sun isa wurin nan da nan, kuma an kai mutane 4 da suka jikkata zuwa asibitin da ke kusa da wurin, cikinsu, akwai mutum guda da ya ji mummunan rauni. Yanzu, sojojin Mali sun cafke mutane da dama.
A wannan rana, gwamnatin Mali ita ma, ta ba da wata sanarwa, inda ta tabbatar da rikicin da aka yi a garin na Gao, ta ce, rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin da wadanda suka jikkata sama da 30.
Amma, wadannan sanarwa guda biyu ba su bayyana game da abin da ya sabbaba rikicin ba. Bisa labarin da wani farar hula da ke garin ya bayar, an ce, Buzaye ne suka kashe wasu Azbinawa guda 3 a ranar 2 ga wata, shi ya sa, a matsayin ramuwar gayya, wasu dakaru dauke da makamai Azbinawa suka kai hari ga motoci guda 2 cike da Buzaye a ranar 6 ga wata.(Bako)