in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Algeri da Mali za su inganta tsaro a kan iyakokinsu
2014-03-09 17:09:20 cri
Ministan tsaron kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga da ke ziyara a kasar Algeria, ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan karfafa hadin gwiwar tsaro da kasar Algeria a kan iyakokinsu, tun bayan da kasarta Algeria ta rufe kan iyakokinta a shekarar da ta gabata, samakakon tabarbarewar yanayin tsaro a arewacin kasar .

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Asabar ga manema labarai bayan ganawarsa da ministan harkokin kasashen wajen Algeria Ramtane Lamamra, inda ya bukaci kasar ta Algeria da ta fara daukar matakan tattaunawa game da batun rikicin da ke faruwa a arewacin kasar Mali.

Ministan na kasar ta Mali ya kuma ce, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar soja da takwaransa na kasar Algeria, kana ya karyaya jita-jitar da ake yayata wa game da batun sace ma'aikatan diflomasiyar Algeria a arewacin Mali a watan Afrilun shekarar 2012.

A watan Janairun shekara da ta gabata ce, kasar Algeria ta rufe kan iyakokinta da Mali sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a arewacin kasar tun bayan da sojojin Faransa da Afrika suka kaddamar da matakan soja da nufin farautar kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China