Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya yi kira ga gwamnatin Mali, da bangarori daban daban wadanda suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta Ouagadougou, da dakaru masu makamai dake arewacin Mali wadanda suka yanke dangantaka da kungiyoyin ta'addacni da yarda da shiga cikin yarjejeniyar ba tare da sharadi, da su cimma matsaya daya ba tare da bata wani lokaci ba kan wata taswirar shawarwari dake budewa ga sassa daban daban dake arewacin kasar, da kuma samu amincewa daga wajensu, domin daidaita matsalar kasar ta hanyar siyasa, ta yadda za a iya girmamawa zaman karko na dogon lokaci, da 'yancin kasa, da dinkuwar kasa, da cikakken yankin kasa.
Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya yi maraba da matakin da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya dauka na nada wani jami'in da zai wakiltarsa a cikin shawarwari na gaba.
A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro kan halin da ake ciki a kasar Mali, inda ministan harkokin wajen Mali ya yi kira ga MDD da kasashen duniya da su kara ba da taimako ga tawagar tabbatar da zaman karko ta MDD dake Mali, ta yadda za ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata. (Danladi)