Sanarwar ta ruwaito wakilin kwamitin kungiyar Red Cross ta kasa da kasa da ke kasar Mali Christoph Luedi na cewa, mambobin kwamitin hudu sun bace, yayin da suke cikin motarsu ta kowawa sansaninsu da ke garin Gao a yankin arewacin kasar Mali.
Mista Luedi ya nuna damuwa kan bacewar abokan aikinsa, tare da bayyana cewa za su yi iyakacin kokari domin gano inda suke.
Inda kuma ya bayyana cewa, ana cigaba da bincike domin gano dalilin bacewarsu, tare da yin kira da tabbatar da tsaron lafiyarsu.
A cikin 'yan shekarun nan, arewacin kasar Mali na fama yawan dakarun dauke da makamai dake sace da yin garkuwar mutanen kasashen yammacin duniya, tare da kashe masu yawon shakatawa da ma'aikatan kungiyoyi masu zaman kansu dake aiki a wurin. (Bako)