Babban wakilin kungiyar AU a kasar Mali da yankin Sahel, Pierre Buyoya ya yi furuci a yayin wani taron manema labarai a gabanin taron kungiyar AU karo na 22 cewa kokarin da gamayyar Afrika ta yi shi ne na maida hankali wajen taimakawa wannan kasa dake yammacin Afrika karfafa zaman lafiya da kuma fuskantar kalubalolin neman ci gaba da take fama da su.
Muna tallafawa kasar Mali yanzu domin fita daga wannan rikici kwata kwata da kuma taimakawa kasar wajen samun ci gaba, in ji mista Buyoya, tsohon shugaban kasar Burundi.
Dukufar da AU ta yi a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika ta hanyar wasu ayyuka misalin tura sojojin gamayyar kasa da kasa, mataki ne da ya samu babban nasara.
A halin yanzu, na yi imanin cewa shekarar 2013 ta kasance mai cike da sarkakiya a kasar Mali. An karbe arewacin Mali daga hannun kungiyoyin kishin islama, yanzu an kafa zarafi mai kyau ga wannan kasa ta samu ci gaba ta fuskar sassanta 'yan kasa da karfafa zaman lafiya. Haka kuma aiwatar da yarjejeniyar Ouagadougou ta shekarar 2013 da aka sanya hannu tsakanin gwamnatin kasar Mali da 'yan tawaye, za ta kasance muhimmin kalubale domin 'yan tawaye har yanzu suna nan, in ji wakilin AU a kasar Mali da yankin Sahel. (Maman Ada)