Jami'in ya ce kasar Amurka za ta ci gaba da gudanar da manufarta ta girke jiragen ruwan yakin kasa kimanin kashi 60 bisa dari a yankin Pacific kafin shekarar 2020, tare da kara karfinta a fannonin tattalin arziki, tsaro, kiyaye muhalli, inganta mu'amala da zaman takewar al'umma, raya dimokuradiyya a yankunan da dai sauransu.
Don gane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Asabar 8 ga wata cewa, kiyaye zaman lafiyar wadannan yankuna, da bunkasar tattalin arzikin yankunan, da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen yankunan sun dace da moriyar kasashen yankunan Asiya da Pacific.
Ya ce kasar Sin na fatan Amurka za ta iya daidaita manufofinta bisa bukatun kasashen yankunan, ta yadda za ta ba da gudumawa wajen kiyaye zaman lafiya, da lumana da kuma bunkasuwar yankunan Asiya da Pacific. (Maryam)