Ranar 8 ga wata, Cheng Guoping, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya ce, bayan da kasar Sin ta zama shugabar taron Asiya na taimakawa juna da tabbatar da amince juna wato CICA a wannan zagaye, za ta yi kokarin ganin taron ya kara taka rawar gani wajen tabbatar tsaron nahiyar Asiya da habaka hadin gwiwa a nahiyar ta Asiya.
Mista Cheng ya fadi haka ne a yayin taron maneme labaru da aka shirya a ma'aikatar harkokin wajen kasar a wannan rana.
Babban taken taron CICA na wannan karo shi ne "Taron CICA, wani muhimmin dandali ne na yin tattaunawa a tsakanin kasashen Asiya, da wanzar da amincewa da juna da kuma taimakawa juna."
Za a gudanar da taron koli na taron na CICA karo na 4 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, inda kasar Sin za ta karbi shugabancin taron a wannan zagaye daga shekarar 2014 zuwa ta 2016. (Tasallah)