in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban Rasha a Sin za ta inganta dangantakar kasashen biyu, in ji ma'aikatar harkokin wajen Rasha
2014-05-16 11:01:02 cri
Jiya Alhamis 15 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Alexander Lukashevich ya bayyana a birnin Moscow cewa, ziyarar aiki da shugaban kasar Vladimir Putin zai kai kasar Sin, za ta ciyar da bunkasuwar dangantakar kasashen biyu gaba.

Mr. Lukashevich ya ce, an kulla dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha ne bisa ka'idojin adalci, abokantaka da kuma fahimtar juna, daga bisani kuma, ake ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban. Hakan ya sa, kasashen biyu suka yi hadin gwiwa yadda ya kamata wajen gudanar da harkokin kasashen BRICS, G20, kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik ta APEC, da kuma kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauran harkokin kasa da kasa.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar tattalin arzikin dake tsakanin kasashen biyu na bunkasa cikin sauri, musamman ma a fannin makamashi, kasashen biyu sun dukufa wajen habaka hadin gwiwar zuba jari wanda ya sa harkokin hadin gwiwar shiyya-shiyya ke bunkasa cikin himma da kwazo.

Bisa gayyatar da shugaba kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Mayu, inda kuma zai halarci babban taron tattaunawa kan inganta cudanya da karfafar hadin gwiwa a nahiyar Asiya na CICA da za a yi a birnin Shanghai na kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China