Shugaban sojojin da ke adawa da gwamnatin kasar Sudan ta Kudu, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya sanar a ran 14 ga wata cewa, za su kai hari birni Juba na kasar da kuma wasu muhimman filayen hakar mai, da zumma tunbuke shugaba mai ci Salva Kiir daga kujerarsa.
A lokacin da yake hira tare da manema labaru a wani kebabben wurin da ke jihar Nile, ya bayyana cewa, Kiir na mulkin kama karya, kuma ba shi da hujjar more ikon mukamin kasar. Idan ba za a kore shi daga mukaminsa ba, ba za'a kawo karshen yakin basasa ba.
Mista Machar ya ci gaba da cewa, yana fatan bangarorin biyu za su girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka daddale a watan Janairu na bana. Kuma yana fatan zai iya yin shawarwari tare da Kiir, fuska da fuska, amma wannan kusan ba zai iyu ba. (Danladi)