A Yau Laraba 16 ga wata, mai magana ga yawun ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana lokacin da take bayani game da halin da ake ciki a sudan Sudan ta kudu.
A gun taron, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, aAkwai rahotanni dake nuna cewa dakaru masu adawa da gwamnatin Sudan ta Kudun suna ci gaba da kai hari a kasar tare da yin gargadin da ga kamfanonin man fetur na kasashen waje da su janye jiki tun da wuri zai yi abin da yasa aka mata tambayar, ko hakan zai yi illa ga kamfanonin Sin?
Madam Hua ta amsa cewa, Sin ta lura da irin wannan labarin da aka bayar. kuma ta dade tana mai da hankali kan yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu wanda a kwanan baya ma bisa kokarin shiga tsakani da kungiyar IGAD da sauransu suka yi, bangarorin na Sudan ta Kudu suka daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Ta ce kasar Sin na fatan za su a bi wannan yarjejeniya yadda ya kamata, tare da bin kokarin shiga tsakani da kungiyar IGAD da sauransu suka yi, na daidaita matsalolin ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.(Fatima)