in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan mata sama da 40 ne suka kubuta daga hannu 'yan Boko Haram
2014-04-20 16:23:18 cri
Mahukuntan jihar Borno dake arewacin Najeriya sun ce 'yan mata sama da 40 ne suka samu kubuta daga hannun dakarun da suka yi awon gaba da su a makon jiya.

Kwamishinan ilimin jihar ta Borno Inuwa Kubo ne ya tabbatar wa manema labaru hakan a garin Chibok. Ya ce tuni aka sada wadannan 'yan makaranta da iyalansu.

Kaza lika Kubo ya ce ya zuwa yanzu 'yan mata 44 ne suka tsira daga cikin su 129, da 'yan bindigar da ake kyautata zaton magoya bayan kungiyar Boko Haram ne suka yi awon gaba da su a farkon makon jiya. Wanda hakan ke nuna sauran 'yan mata 85, da kawo yanzu ba a kai ga samo su ba tukuna.

Rahotanni daga jihar dai na cewa jami'an tsaro da wasu mafarauta na ci gaba da neman ragowar 'yan makarantar da aka sace.

Tun da fari 'yan mata 4 sun samu kubuta daga maharan, a yammacin ranar da aka sace su, yayin da motar da suke ciki ta samu matsala a hanya. Sai kuma wasu su 10, da aka ce sun samu tsira a ranar Larabar da ta gabata.

Yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda ragowar 'yaran suke, gwamnan jihar ta Borno Kashim Shettima, ya nanata kira ga daukacin masu gudanar da wannan aiki, da su dukufa wajen tabbbatar da samun nasarar ceto 'yan makarantar ba tare da wani jinkiri ba.

Bugu da kari gwamnan ya kuma sanya tukwuicin naira milyan 50 ga duk wanda ya gabatar da bayani mai amfani, da zai taimaka wajen gano inda ragowar wadannan 'yan mata suke.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace 'yan makarantar, ko bayyana kudin fansa a kan su ba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China