in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Li Keqiang a kasashen Afirka ta jawo hankalin kafofin yada labaru na kasashen waje
2014-05-09 17:11:41 cri

Ranar 4 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya fara ziyarar aiki a kasashen Habasha, Nijeriya, Angola da Kenya. Wannan shi ne karo na farko da ya ziyarci kasashen Afirka tun bayan da ya zama firaministan kasar Sin. Kafofin yada labaru na waje suna ganin cewa, ziyararsa, wani muhimmin mataki ne da sabuwar gwamnatin kasar Sin ta dauka a fannin diplomasiyya, wanda ya bayyana muhimmin matsayin da kasashen Afirka ke dauka a harkokin diplomasiyyar kasar Sin.

A cikin sharhin da tashar Intanet ta All Africa ta rubuta a ranar 8 ga wata, ta ce, kasashen Sin da Afirka na son yin kokari tare wajen inganta hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki tare da inganta kokarinsu na samun nasara tare.

Sa'an nan mista Li Keqiang ya halarci taron tattalin arziki na duniya da aka gudana kan Afirka a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, inda kuma ya ba da wani jawabi mai lakabin "hada kai wajen inganta bunkasuwar kasashen Afirka". Dangane da haka, kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce, a cikin jawabinsa, Li Keqiang ya jaddada cewa, kamar ko da yaushe, Sin za ta dada agajin da take baiwa nahiyar Afirka, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ba, ya kuma sake nanata cewa, kasar Sin ba za ta tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen Afirka ba, kuma ba za ta tilasta wa kasashen Afirka yin wani abu ba.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China