Firaministan kasar Sin, Li Keqiang ya yi amanna cewa, zai karfafa huldar gamayya da kasashen Tanzania da Benin a fannoni daban daban.
Li ya yi wannan alkawari ne a yayin taruka daban daban da ya gudanar da shugaban kasar Tanzania, Jakaya Kikwete da kuma shugaban kasar Benin, Thomas Boni Yayi wadanda su ma suna a Abuja, babban birnin kasar Najeriya a halin yanzu, domin halartar taron tattalin arziki na duniya a kan Afrika na shekara ta 2014, wanda ake gudanarwa a Nigeriya.
A yayin da yake ganawa da shugaban kasar Tanzania, Li ya ce, kawancen kasar Sin da Tanzania wani ginshikin abu ne da ya shafi hulda tsakanin kasar Sin da Afrika, a inda Li ya kuma yaba da yadda kasashen biyu a kan suke amincewa, tare da taimakon juna a tsawon shekaru hamsin da suka wuce, tun bayan da suka kulla huldar jakadanci.
A nashi bangaren, shugaban kasar ta Tanzania, Kikwete ya kira kasar Sin, a matsayin abokiyar arziki ga Tanzania da kuma Afrika, a inda kuma ya lura da cewar, tsarin dangantaka wanda Li ya ba da shawarar da a samar da shi, a cikin jawabinsa a babbar hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika AU a ranar Litinin, ya yi daidai da bukatun jama'ar Afrika, kuma yana da goyon bayan kasashe da dama na Afrika.
A yayin da firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Benin Boni Ya yi, ya ce, hulda tsakanin kasashen Sin da Benin sai kara kaimi take yi, kuma ya yi fatan dukanin bangarorin biyu za su ci gaba da gudanar da ayyukan samar da ababen inganta rayuwa sannu a hankali, tare da fadada dangantaka a fannonin tattalin arziki da cinikayya domin daukaka dangantakar su.
Shugaban kasar ta Benin ya ce, yana daukar kasar Sin a matsayin abokiya ta kut-da-kut, kuma agajin da kasar Sin take badawa a wajen gina hanyoyi da samar da tashoshin makamashi ya taimaka wajen zaburar da ci gaban kasarsa, hakan, in ji shi, ya kuma taimaka wajen habbaka bunkasar yankin na Afrika. (Suwaiba)