in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arziki da al'adu manyan jigon hadin gwiwa ne tsakanin Sin da Afrika
2014-05-07 09:58:09 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang a ranar Talatan nan kafin ya tashi daga kasar Habasha ya ce, tattalin arziki da hadin kai a bangaren al'adu su ne manyan jigo na huldar dake tsakanin kasarsa da nahiyar Afrika.

A wani taron ganawa da ya yi da manyan 'yan kasuwa na nahiyar da wakilai daga fannoni ilimi da al'adu, firaministan na Sin ya ce, tattalin arziki da ciniki, sannan aka hada da al'umma da al'adun su hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika sun hade wuri daya, ta yadda ba za a iya raba daya biyu ba. Ya lura da cewa, ci gaba a wadannan fannoni daga dukkan bangarori shi ke kara hada zumunci.

Mr. Li ya ce, Sin da Afrika gaba daya suna da al'umma biliyan 2.3, daya daga cikinsu wato Sin ta samu cigaba mai armashi, daya kuma Afirka na da cikakken fata na samun cigaba ba da dadewa ba. Don haka ya ce, Sin da Afrika suna kallon junan su a matsayin wata gada da kowane zai samu dimbin cigaba, kuma suna moriya daga hadin gwiwwar dake tsakaninsu na tsawon lokaci yanzu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China