in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Afirka sun darajanta jawabin da Li Keqiang ya gabatar a hedkwatar AU
2014-05-07 10:54:37 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi wani jawabi mai taken "samar da wata kyakkyawar makoma ga hadin kan Sin da Afirka" a ranar 5 ga wata a hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Game da haka, masanan Afirka sun bayyana cewa, shawarwarin da Li ya gabatar ciki har da ciyar da manyan ayyuka 6 gaba, kyautata dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, daga matsayin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, sun samu karbuwa sosai daga kasashen Afirka.

Mazanarcin harkokin siyasa na kasar Sudan Mohammed Hasan Said ya yi nuni da cewa, jawabin Li na bisa tushen gaskiya, inda aka gabatar da wasu ka'idoji, da tunani, da cikakken shiri dangane da inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, ganin cewa mista Li ya gabatar da fannonin da bangarorin biyu zasu hada kai a nan gaba.

A yayin da wani kwararre na kasar Zimbabwe Johnson ya ce, jawabin Li ya shigar da sababbin batutuwa cikin hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, kuma daga matsayin hadin kai shi ne burin nahiyar Afirka cikin dogon lokaci.

Tsohon jakadan Masar da ke Sin Ahmed Rezk ya ce, jawabin da Li ya bayar na kunshe da manyan batutuwa masu yawa, abin da ya fi muhimmanci a cikin jawabinsa shi ne, shugabannin Sin za su ci gaba da nuna goyon baya ga neman cigaban nahiyar Afirka.

Kwararre kan harkokin cigaba na kasar Zambiya Fred Sumter ya ce, sabuwar hanyar da za a bi wajen hadin kai a tsakanin Sin da Afirka bisa jawabin Li, ta kasance wata kyakkyawar dama ga kasashen Afirka. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China