in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Habasha
2014-05-06 20:52:23 cri

A yau Talata 6 ga wata da safe agogon Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Mulatu Teshome.

A yayin ganawar, mista Li ya ce, kasar Sin na son inganta dankon zumuncin da ke tsakaninta da Habasha, habaka da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da suka hada da shimfida hanyar dogo da hanyar mota, da kuma ayyukan kera kaya, da kyautata hadin gwiwarsu a hada-hadar kudi da gina filayen raya masana'antu, a kokarin raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 zuwa sabon mataki.

A nasa bangaren, Mulatu Teshome ya nuna godiya ga goyon bayan da Sin ke nuna wa kasarsa da taimakon da take bayarwa da kuma shiga a dama da su da masana'antun kasar Sin suke yi, wadanda suka kara azama kan bunkasuwar kasarsa ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Habasha ta yaba wa nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin ci gaban kasa, kuma tana son yin koyi da kasar Sin da kuma habaka hadin gwiwa da kasar Sin a ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a. Ya kara da cewa, Habasha na maraba da masana'antun kasar Sin da su kara zuba jari da gudanar da cinikayya a Habasha, hakan zai sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin Habasha da kuma samun nasara tare. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China