Kasar Sin da nahiyar Afrika sun cimma muhimmin matsaya game da karfafa hadin gwiwwa dake tsakanin su akan ayyukan rage radadin talauci, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwar hadin gwiwwa a kan matsayar da aka cimma yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ke ziyarci cibiyar kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU dake birnin Adis Ababa na kasar Habasha.
Sanarwar da aka fitar a ranar Litinin yayin ziyarar firaministan na Sin a cibiyar AU ta nuna cewa, Sin da Afrika a shirye suke a ko da yaushe su karfafa kokarin da suke yi wajen rage talauci, sannan kuma su tsaya tare su fuskanci kalubalen da ka iya bullowa sakamakon wannan kokarin nasu.
Har ila yau sanarwar ta lura da cewa, ayyukan rage talauci na da muhimmanci ga kasashen Sin da na nahiyar Afrika, kuma za su kawo moriya a gare su duka, inda aka hada gwiwwa domin inganta tushen da aka dasa mai karfi. (Fatimah)