Sannan, Mr. Li Keqiang ya kai ziyara ga wani yankin raya masana'antu da wani kamfanin kasar Sin ne ya zuba jari ya gina a kasar Habasha, inda aka riga aka shigar da kamfanoni 19 wadanda suke samar da guraban aikin yi da yawa ga mutanen kasar Habasha.
Bisa ajandar da aka tsara, yau da yamma, Li Keqiang, firaministan kasar Sin zai tashi daga Addis Ababa na kasar Habasha zuwa birnin Abuja na kasar Najeriya domin fara ziyararsa ta aiki a kasar ta kwanaki 3. (Sanusi Chen)