in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin na kambama fasahohin jiragen kasa da na sama a Afrika
2014-05-06 11:01:06 cri

A wani katafare zauren taro dake hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika AU a Addis Ababa, an jera wasu samfarin jiragen kasa guda 4 kirar kasar Sin, daya daga cikin jiragen kasa jirgi ne mai tsananin sauri. A dai cikin wannan azure, akwai kuma samfurin jiragen sama guda 10 kirar kasar Sin, wadanda aka jera su tun daga ranar Litinin.

A tare da firaministan kasar Sin Li Keqiang, wanda ya fara ziyarar shi ta Afrika, akwai kuma firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn da kuma shugabar hukumar hadin kan tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma wadanda suka halarci baje kolin, wanda yake nuni da fasahohi na zamani, dake tashe yanzu a fannin jiragen kasa da kuma na sama.

Shugabannin sun kuma kalli wani fim na bidiyon, wanda aka nuna akan wani babban bango. Shi dai fim din ya nuna ci gaban da aka samu a masana'antun jiragen kasa da na sama na kasar Sin. Tun farko sai da masu ilmin fasaha na kasar Sin suka zagaya da shugabannin, tare da yi masu bayani akan samfur din jiragen kasa da na sama da aka jera da kuma ba su cikakken bayani akan yadda suke aiki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China