in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara kada kuri'un babban zaben Afirka ta Kudu a ketare
2014-04-30 14:54:32 cri
A ranar 29 ga watan nan ne aka fara kada kuri'un zagayen farko na kujerun majalisun dokokin kasar Afirka ta Kudu a ketare.

Hakan dai na nuna cewa an kaddamar da wannan zabe a hukunce, inda masu kada kuri'u dake wajen kasar kimanin dubu 26 suka fara jefa kuri'unsu a wasu tashoshin kada kuri'u da aka kafa a birane 123 cikin kasashen duniya daban daban.

Rahotannin sun bayyana cewa, bayan kammala jefa kuri'un a ketare, za a like dukkan kuri'un cikin akwatunan zabe, a kuma yi jigilar su zuwa fadar mulkin gwamnatin kasar dake birnin Pretoria, inda za a lasafta su tare da kuri'un da aka kada a gida bayan kammala kada kuri'un baki daya.

Za dai a gudanar da babban zaben Afirka ta Kudu ne a daukacin fadin kasar a ranar 7 ga watan Mayu, a karo na biyar da kasar za ta gudanar da babban zabe, tun bayan kawar da tsarin nuna wariyar launin fata a shekarar 1994.

Bisa wani sabon bayanin da aka fidda game da ra'ayoyin jama'a a ran 20 ga wata, akwai alamun dake nuna cewa jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ce za ta samu goyon bayan kimanin kaso 65 bisa dari na masu kada kuri'un, yayin da aka yi hasashen jam'iyyar adawa ta kawancen domokuradiyya, za ta samu goyon bayan kimanin kaso 23 bisa dari na masu kada kuri'un. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China