Yan sanda a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, sun ce, aikin da ake yi na ceto rayukan wasu masu aikin hakar zinari ba bisa ka'ida ba, na fuskantar kalubale, sakamakon kin yarda da wasun suka yi na fitowa don tsoron fuskantar hukunci.
Ya zuwa ranar Litinin dai, an samu nasarar fiddo mutane 22, cikin mutane da dama da ake zaton na makale a wani bangaren mahakar dake gabashin birnin na Johannesburg. Yayin da kuma wasu da ake zaton na can kasan mahakar kimanin su 200 suka ki yarda a fito da su.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, masu aikin ceton sun aika sako ga wadanda suka ki yarda su fito, cewa za a like bakin mahakar a ranar 3 ga watan Maris dake tafe, ko da yake kawo yanzu ba a tabbatar da ko wannan barazana za ta tilasawa mutanen yarda su fito ba.
Da yawa daga 'yan kasar Afirka ta Kudu dai na shiga wannan sana'a ta hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, a matsayin hanyar neman rufin asiri, duk kuwa da hadarin da hakan ke tattare da shi ga rayukansu. (Saminu)