in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin shekarar Afirka ta Kudu a birnin Beijing
2014-04-30 09:37:36 cri

A ranar Talata 29 ga watan nan na Afirilu ne aka kaddamar da bikin shekarar Afirka ta Kudu a kasar Sin. Bikin wanda aka bude a nan birnin Beijing na kunshi da shirye-shirye na tsahon shekara guda, zai kuma ba da damar baje kolin al'adu da managartan dabi'un al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu.

Bisa tsarin bikin dai, za a gudanar da shirye-shirye daban daban da suka shafi kasar kimanin 50, ciki hadda tarukan karawa juna sani game da harkokin cinikayya, da ilimi, da dai sauran su.

Tuni dai shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin, da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma, suka aikewa junan su sakon taya murnan zuwan wannan biki.

A jawabinsa yayin kaddamar da bikin, mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Jianchao, ya ce, shagulgulan da za a yi, masu kunshe da al'adun kasashen biyu a wannan karo, za su dada habaka kyakkyawar dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. Ya ce, bikin na wannan lokaci zai ba da cikakkiyar dama ga al'ummar Afirka ta Kudu, wajen nunawa Sinawa tarin al'adun su, da ma dankon zumunta da hadin gwiwar da ke tsakanin sassan biyu.

Yayin ziyarar da shugaba Xi ya kai kasar Afirka ta Kudu a bara ne dai shuwagabannin kasashen biyu, suka daddale yarjejeniyar gudanar da bikin shekarun kasashen nasu. Inda bisa yarjejeniyar, baya ga bikin Afirka ta Kudu a nan kasar Sin na bana, za kuma a gabatar da bikin Sin a Afirka ta Kudu a shekarar 2015 mai zuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China