An kafa wani mutum-mutumin tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela a ranar Litinin a gaban majalisar dokokin kasar Afrika ta Kudu dake birnin Cape Town a yayin da kasar take bikin zagayowar shekaru ashirin da samun 'yancin fadin albarkacin baki.
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya gabatar da wannan mutum-mutumin a yayin bikin a gaban idon shugaban majalisar dokokin kasar Max Sisulu, shugaban kwamitin kasa na gundumomin kasar, mista Mninwa Mahlangu, mambobin gwamnatin kasar, mambobin iyalan marigayi Mandela da sauran manyan mutane, har ma da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Frederic de Klerk, wanda tare da Nelson Mandela ya taimaka wajen kawo karshen wariyar launin fata a Afrika ta Kudu.
Za mu cigaba da bin hanyar da Madiba ya shata, da kuma giramama gadonsa, in ji shugaba Zuma, tare da bayyana cewa, wannan mutum-mutumin na nuna yadda aka samu cigaban tsarin demokaradiyya a kasar Afrika ta Kudu a cikin gajeren lokaci. (Maman Ada)