Babban kamfanin nan da ke samar da ma'adinan platinum mafi girma a duniya (Amplats) yana tabka asarar da ta kai dala miliyan 9.3 kwatankwacin kudin kasar Afirka ta Kudu wato kimanin rands miliyan 100 a ko wace rana, sakamakon yajin aikin da ma'aikatan hakar ma'adinan kasar ke yi.
Kakakin kamfanin Mpumi Sithole ne ya bayyana hakan ranar Litinin, inda ya ce, kamfanin yana asarar yawan ma'adinan da ya kai oz 4000 wato kimanin rands miliyan 100 na kudin shiga a ko wace rana.
Yajin aikin wanda ya shiga makonni na 4 ba tare da wata alamar kawo karshen sa ba, ya kusa kai ga durkusar da kamfanin da ke kan gaba wajen hakar ma'adinai a duniya. Bugu da kari, yajin aikin wanda kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinan kasar (AMCU) ta shirya, ya shafi wasu kamfanonin hakar sinadarin platinum guda 2, wato Lonmin da Impala.
A ranar Litinin ne dai hukumar sasantawa da sauraron koke-koken ma'aikatan kasar (CCMA) ta dawo tattaunawa da kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinan kasar (AMCU) da nufin kawo karshen yajin aikin ma'aikatan bayan da aka gaza cimma nasara a tattaunawar da suka gabata, duk da cewa, kamfanin na Amplats ya shigar da hukumar kara a ranar Asabar saboda asarar da kamfanin ya ce ya tabka sakamakon yajin aikin. (Ibrahim)