in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ceto mahakan da suka makale a karkashin kasa a Afirka ta Kudu
2014-02-17 10:57:13 cri

Masu aikin ceto a kasar Afirka ta Kudu, sun bayyana a ranar Lahadi 16 ga wata cewa, an ceto mahaka 11 cikin sama da mahaka 200 da ke hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da suka makale a wata tsohuwar mahakar zinare a kusa da Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Bayanai na cewa, mahakan sun makale ne bayan da ake zargin wasu abokan aikinsu sun kwace masu zinaren da suka hako ranar Asabar da rana a mahakar zinaren nan ta Gold One shaft da ke Benoni a gabashin birnin Johannesburg.

Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ER24, Werner Vermaak ya ce, yanzu haka, ana duba lafiyar mahakan da aka ceto, kana babu wani rahoto game da wanda ya jikkata.Yanzu haka jami'an hukumar kula da bala'u da bayar da agajin gaggawa na kasar suna wurin da lamarin ya faru.

Wannan lamari na nuna karuwar hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a kasar ta Afirka ta Kudu. Ko da a watan Maris na shekarar 2012, a kalla masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba 20 ne suka mutu a karkashin kasa a lardin Gauteng da ke gabashin kasar.

Kana a farkon shekarar da ta gabata, an ceto wasu 40, bayan da suka makale a karkashin kasa a yammacin birnin Johannesburg.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China