An zartas da hakan ne yayin babban taron kungiyar tarayyar kasashen Turai na bazara da ya gudana a birnin Brussels ran 20 ga watan nan. Inda yanzu haka wasu karin jami'an Rashan 12 za su fuskanci takunkumin da aka sanyawa kasar tasu, baya ga dauke babban taron kungiyar ta EU da aka yi daga Rasha.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana a ran 22 ga wata cewa, bai dace EU ta tsai da irin wannan kuduri ba, kuma kasar Rasha na fatan a dawo da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu ta hanyar da ta dace da moriyar juna.
Bisa rahotannin baya bayan nan, da kafofin watsa labarai na kasar Rasha ke fitarwa, an ce shugaba Vladimir Putin na Rasha ba zai halarci babban taron tsaron makamashin nukiliya da za a yi a birnin Hague ba, a maimakon haka, ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov zai halarci taron a matsayin shugaban tawagar wakilan Rashan.
A wani ci gaban kuma, firaministan kasar Ukraine Arseniy Yatsenyuk, ya gana da babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a birnin Kiev ranar 22 ga watan nan, inda Mr. Yatsenyuk ya nanata cewa, kasar Ukraine ba ta amince da kuri'ar raba gardama da Crimea ta yi ba. A hannu guda Mr. Ban ya nuna cewa, ziyararsa a wannan gaba, na da manufar goyawa gwamantin kasar da jama'ar ta baya ne, musamman a irin halin da ake ciki yanzu.
Bugu da kari, a dai wannan rana ne kasashen Rasha da Faransa, suka fidda sanarwa, mai kunshe da fatan cewa, ya kamata kungiyar tsaron hadin gwiwar Turai ta aike da tawagar sa ido kasar ta Ukraine, don ba da taimakon sassauta rikicin kasar. (Maryam)